YANZU-YANZU: Majalisar Zamfara ta tsige Mataimakin Gwamnan jihar, Mahdi

Majalisar Dokoki ta Jihar Zamfara ta tsige Mataimakin Gwamna, Mahdi Aliyu Gusau.

A zaman majalisar na yau Laraba, ƴan majalisa 20 cikin 21 ne su ka zaɓi a tsige Mataimakin Gwamnan bayan da a ka miƙa ƙudurin cire shi ɗin.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a jiya Talata ne dai kwamitin bincike da a ka kafa domin tuhumar Mahdi ɗin ya zauna jiya, amma kuma Mataimakin Gwamnan bai halarci zaman ba.

Sai dai kuma bayan da kwamitin ya miƙa rahoton da gaban majalisar a yau, sai mambobin su ka zaɓi su tsige Mataimakin Gwamnan.

Ƙarin bayani na nan tafe…

Click Here To Drop Your Comment