News

Yanzu-Yanzu Wasu Matasa Dauke Da Makamai Sun Rushe Masallatai 2 A Jos Tare Da Kone Shaguna 14

‘Masallatai 2 A Jos Tare Da Kone Shaguna 14

Wasu Matasa Dauke Da Makamai Sun lalata masallatai biyu, sun sace tare da kona shaguna 14 a kasuwar kayan gini na karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato.

Kasuwar Dai ta ƙunshi ɓangaren kayan masarufi, gami da kayan lambu. Shugaban kungiyar masu sayar da kayan lambu, a jihar, Dalyop Pwasa, ya tabbatar wa DAILY NIGERIAN faruwar lamarin.

“Na’am gaskiya ne cewa wasu mutane sun shiga cikin kasuwarmu a ranar Laraba, sun karya wasu shaguna, sun sace kayayyaki sun kona shaguna 14. Mr Pwasa ya kara da cewa “Sun kuma lalata masallatai biyu a kasuwa.”

Da yake tabbatar da Mista Pwasa, sakataren kungiyar kasuwar, Fodio Umar, ya ce an rushe masallatan biyu gaba daya duk da dokar hana fita. Malam Umar ya ce sun kuma yi awon gaba da kayan shagunan su tare da kona shaguna da dama.

A cewarsa, an kai rahoto ga rundunar ‘yan sandan yankin da ke Sabon Barki, inda suka nemi limaman masallatan guda biyu su kai rahoto ofishin.

“Mista Dalyop Pwasa yana yin iya bakin kokarin sa. Yana tara manyan motocin da suka kwashe kayanmu da yawa daga kasuwa.

Ya kara da cewa “Shi ne ya kira masu kashe gobara da suka kashe wutar.

Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, ASP Ubah Ogaba, bai amsa kiran wakilin wakilinmu ba kuma bai amsa sakon tes na neman amsa‘ yan sanda kan lamarin b


 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button