News

Yanzu-Yanzu Yan Biafra Sunyiwa Wasu Fulani Makiyaya Yankan Rago A Jahar Anambra

Wasu Mutane da ake zargin mambobin kungiyar ‘yan Biafra ne, Wato IPOB, sun yanyanka Fulani makiyaya Goma Sha Tara 19 a yankin Igbariam na karamar hukumar Oyi da ke Jihar Anambra.

 

Kamar Yadda Jaridar Daily Nigerian Ta Rawaito Cewa. yan qungiyar biafran Sun mamaye wani bene mai hawa inda Fulani makiyaya ne ke zaune a yankin da misalin karfe 2 na safiyar Ranar Lahadi.

 

Masu aikata laifin sun kashe mata 12, dakuma maza bakwai da yara kana da ba a bayyana adadinsu ba.

Ana zargin cewa masu laifin sun fito da wadanda aka kashe din,

Sannan suka yi musu tsirara, tare da daure musu hannaye sannan suka yanyanka su.

Wakilinmu Daily Nigerian ya samu wasu hotunan gawarwakin wadanda Akaiwa Kisan Gillan. A cikin wadannan hotunan, an rasa wasu muhimman sassan jikin wadanda aka kashe din,

Kakakin rundunar ‘yan sanda reshen jihar Anambara, Ikenga Tochikwu, bai amsa kiran da wakilin daily nigerian ya yi masa ta layin wayarsa ba har zuwa lokacin rubuta wannan rahoton.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button