Politics

Babu Wata Najasa A Takalmin Osinbajo Dan Ya Shiga Masallaci Dashi. Sheriff Almuhajir yayi fatawa akai

Wa Yace Akwai Najasa A Takalmin Osinbajo?

Babu Wata Najasa A Takalmin Osinbajo Dan Ya Shiga Masallaci Dashi. Sheriff Almuhajir yayi fatawa akan shigar Osinbajo Masallaci da takalmi asha karatu lafiya.

Shin takalmi aka hana shiga masallaci ko najasa aka hana shiga masallaci, waye ya gaya ma ku cewa takalmin Osinbajo akwai najasa a cikin shi. Shin menene banbancin takalmi mai tsarki da hula mai tsarki?

Muddun idan babu najasa a zahirin takalmin Osinbajo babu wanda ya ji wari, ko ya ga alamar ruwa mara tsarki, to takalamin daidai ya ke da rigar jikan limamin masallacin, domin sharadin tufafi duka shine tsarki.

Ya kamata mutane su rika tambaya kafin su kawo zantukan da za su rika tunzura al-ummah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button