Religion

BIDIYO: Masha Allah Yadda Dalibai Kusan Dubu 1 Sukayi Murnar Haddace Al-Qur’ani Mai Girma A Kano.

BIDIYO: Masha Allah Yadda Dalibai Kusan Dubu 1 Sukayi Murnar Haddace Al-Qur’ani Mai Girma A Kano.

Kimanin dalibai 868 ne sukayi bikin murnar haddace Alku’ani mai girma a ranar Lahadin da ta gabata a jihar Kano.

Bikin ya kasance na daban da ya shiga tarihi a jihar nan da ma kasa baki daya, duba da irin tarin daliban da suka sami damar haddar AlQur’ani.

Cikin dalibai 868 akwai Maza 284 da Mata 584 dukkaninsu yan kasa da Shekara 25.

Daliban sun sami damar haddace littafin Allah ne a karkashin wani shiri na musamman na makarantar marigayi Sheikh Khalifa Ishaq Rabiu.

Marigayi Khalifa Ishaq Rabiu dai ya yi fice wajen hidimtawa addinin musulunci dama musamman littafin AlQur’ani da malaman Qur’ani a kasar nan.

Bayan rasuwarsa kuma Iyalansa sun dora da aikin da yakeyi, abinda ya bada damar yaye wadannan tarin dalibai da suka haddace Alqur’ani.

📷 Bluelens

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button