Politics

BIDIYO: Wasu ‘yan daba sun mamaye rumfunan zabe a Legas, sun banka wa akwatin zabe wuta

BIDIYO: Wasu ‘yan daba sun mamaye rumfunan zabe a Legas, sun banka wa akwatin zabe wuta

‘Yan daba da dama sun yiwa wasu rumfunan zabe kawanya a yankin Oshodi da Itire dake Legas inda suka banka wa wasu takardu da akwatuna wuta.

‘Yan  daba wadanda dukkansu sanye da bakaken kaya da rufe fuska, sun isa yankin ne da misalin karfe 11:30 na safiyar yau asabar.

Wasu masu kada kuri’a, wadanda ba su iya guduwa ba lokacin da ‘yan  daba suka iso sun ji rauni.

Majiyoyi sun ce ‘yan  daba, daga baya sun zagaya yankin, mintuna kadan bayan wasu jami’an tsaro da ke aikin zabe sun bar aikinsu.

A cewar Tajudeen Haruna, bayan mintuna kadan ne ‘yan   daba suka bude wuta tare da tsorata masu kada kuri’a.

“Daga baya ne ‘yan  daba suka cinna wa akwatin zabe da wasu kayayyaki wuta,” in ji shi.

Hakazalika, wasu ‘yan banda sun kai farmaki yankin Itire, da misalin karfe 12, inda suka tsorata masu kada kuri’a daga sassa daban-daban na yankin.

Hakazalika, wasu ‘yan banda sun kai farmaki yankin Itire, da misalin karfe 12, inda suka tsorata masu kada kuri’a daga sassa daban-daban na yankin.

A halin da ake ciki, akwai dimbin sojoji da ‘yan sanda a cikin birnin Legas don dakile tabarbarewar doka da oda.

A lokaci guda kuma, samari sun mayar da hanyar motar Agege da Apapa-Oshodi, Okota da wasu sassa na fadar Ago hanyar zuwa filin wasan kwallon kafa.

Ana kuma samun tashin hankali a mafi yawan yankunan Ago, Isolo da Ire-Akri biyo bayan gazawar wasu masu kada kuri’a wajen gano wuraren zabensu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button