Politics

Cigaba Da Gina Jihar Borno Ya Fimin Zama Mataimakin Shugaban Kasa -Zulum

Cigaba Da Gina Jihar Borno Ya Fimin Zama Mataimakin Shugaban Kasa -Zulum

Gwamnan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya Babagana Umara Zulum ya lashe zaben fidda gwanin jihar da aka yi, ya kuma yi watsin da masu yi masa ta yin ya nemi mataimakin shugaban Najeriya.

Babagana wanda shi kadai ne dan takarar a karkashin jam’iyyar APC ya lashe zaben ba tare da hamayya ba, wanda hakan zai ba shi damar karawa da takwarorinsa na sauran jam’iyyun a zaben 2023.

An yi zaben fidda gwanin ne a cibiyar wasanni ta El-Kanemi da ke Maiduguri a yammacin ranar Alhamis, kuma manyan ‘yan jam’iyyar APC sun halarci zaman ciki har da tsofaffin gwamnonin jihar da suka hada da Kashim Shettima da Ali Modu Sheriff da kuma Maina Ma’aji Lawan.

Ministan noma Mustapha Baba Shehuri da tsohon dan majalisar dattijai kuma Ambasadan Najeriya a China Baba Ahmed Jidda duk suna cikin mahalarta taron.

Uba Maigari Ahmadu wanda shi ne shugaban zaben fidda gwanin gwamnonin da na ‘yan majalisa jihar Bornon ya sanar da cewa Zulum ya lashe zaben ne da kuria 1,411.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button