Religion

Innalilillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un Mahaifiyar Limamin Masallacin Al-Furqan, Dakta Bashir Aliyu ta rasu

Mahaifiyar Limamin Masallacin Al-Furqan, Dakta Bashir Aliyu ta rasu

Mahaifiyar fitaccen Malamin addinin musuluncin nan na Jihar Kano, Dakta Bashir Aliyu Umar ta rasu.

Marigayiyar, mai suna Hajiya Khadija Aliyu Harazumi ta rasu da safiyar yau Talata a gidanta da ke Gwale Gudundi bayan ta yi rashin lafiya.

Hajiya Kahdija daya ce daga cikin matan Dan Amar Kano Alhaji Aliyu Harazumi Umar.

Ta rasu ta bar ƴaƴa da jikoki da dama.

Daga ciki akwai babban limamin masallacin juma’a na Al-Furqan da ke unguwar Nasarawa a birnin Kano Dr Bashir Aliyu Umar

Haka kuma za a yi jana’izarta a Kofar Kudu da ke gidan Sarkin Kano da misalin ƙarfe 3 na yamma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button