Religion

Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo dan wiwi ne wanda bai san mutuncin kansa balle ya san mutuncin wani,

HAKIKA FITINA WUTAR DAJI CE…

Shugaban Majalisar Malaman kungiyar Izala na duniya Ash-sheikh Muhammad Sani Alhaji Yahya Jingir (H) ya kwatanta Babban Malami Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo (H) a matsyain ‘Dan wiwi saboda fahimtar da yake yadawa akan makomar iyayen Annabi (SAW)

Sheikh Sani Yahaya Jingir yace Sheikh Ibrahim Jalo Jalingo dan wiwi ne wanda bai san mutuncin kansa balle ya san mutuncin wani, yana hada husuma da raba kan Musulmai, inji Dattijon Malami Sheikh Sani Yahya Jingir

Abu na farko banji dadi da Sheikh Sani Yahya Jingir ya fito ya bayyana wa duniya cewa Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo Dan Wiwi ne, hakan bai kamata ba ko da ya tabbata Malamin yana shan wiwi

Abu na biyu Sheikh Dr Ibrahim Jalo mutumin kirki ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa akan yada addinin Allah, sannan baya jin tsoro ko shakkar mayar da raddi ga kafurai da wadanda suke yakar Musulunci, sannan Malami ne mai tsananin gudun duniya

Abu na uku: Fatawar da Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo yake yadawa akan makomar iyayen Annabi (SAW) fahimtarsa ne haka wanda ya gani a cikin Littafin Hadisi, bai taba fadin ra’ayinsa ba, ba da jahilci yake magana ba

Abu na hudu: Sheikh Dr Ibrahim Jalo Jalingo baya yiwa Musulunci da Musulmai adalci akan wannan mas’ala da bata da wani amfani da dadin ji wanda Malaman duniya sukayi ittifakin cewa ba’a tattaunata a gaban jahilai, mas’alace da ake tattaunawa a gaban daliban ilmi, su ma Daliban sai karatu ne idan ya biyo ta kai kafin sai a bayyana fahimtar Malamai a wuce gurin da gaggawa

Abu na biyar: Malaman duniya tun daga na farkonsu har zuwa yau sun rinjayi Malaman da suke ganin iyayen Annabi suna wuta, mafi yawan Malamai sun tafi akan fahimtar iyayen Annabi (SAW) ‘yan Aljannah ne

Abuna shida: Wannan fatawar da Dr Ibrahim Jalo ke yadawa bata da wani amfani sam, ba abinda zata haifar sai fitina da tashin hankali da rarrabuwar kai da kuma tsana, don haka indai yana halin lafiya kalau to ya kamata ya hakura ya dena tado da ita, imba haka ba har ‘ya’yan da ya haifa zasu iya tsanarsa

Abu na bakwai: Shawarace, wannan muguwar fahimta marar dadin ji, tunda a Facebook ake yadawa, ya kamata a guji duk wanda yake da irin wannan fahimta yana yadawa, cewa iyayen Annabi suna wuta, ina nufin a fara blocking dinsu, da yin unfollowing dinsu, saboda maganar bata da dadin ji, tana bakanta rai da kuma girgiza zuciya

Wallahi ana daukar alhakkin mu akan yada wannan bakar fahimta, Wallahi rayukan mu fansa ne ga Annabi (SAW) da iyayensa

Ina jin tsoro kar Dr Ibrahim Jalo yayi sanadi na haddasa fitina da yaki a tsakanin Musulmai, Ya kamata Shugaban Kungiyar Izala na duniya Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau da tawagarsa su yiwa tufkar hanci kafin lokaci ya kure, domin muna jin furucin jahilai daga cikin mu

Allah Ya sauwake

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button