Politics

Yanzu-yanzu: Kwankwaso da Shekarau sun shiga ganawar sirri

Yanzu-yanzu: Kwankwaso da Shekarau sun shiga ganawar sirri

An shiga ganawar sirri tsakanin tsohon Gwamna Engr. Rabi’u Kwankwaso da Sanata Malam Ibrahim Shekarau yanzu haka a gidansa da ke Munduɓawa.

Kwankwaso ya ziyarci Shekarau tare da muƙarrabansa da sauran ƴan jam’iyyar NNPP.

Kafin shiga tattaunawar sai da Kwankwaso da Shekarau suka gabatar da jawabai na nuna sun haɗu waje guda.

Daga bisani Malam Shekarau ya sanar da cewa za su yi ganawar sirri.

Magoya bayan tsoffin Gwamnonin biyu sun cika maƙil a gidan yayin da ake shirin taron karɓar Shekarau a NNPP gobe Laraba.

Hoton da ke ƙasa kuma an kafa shi ne a kwanar shiga gidan Malam Shekarau.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button