Politics

YANZU-YANZU: Tshohon Gwamnan Jahar Kano Sanata Kwankwaso Ya fice daga PDP, watakila ya koma ADC

YANZU-YANZU: Tshohon Gwamnan Jahar Kano Sanata Kwankwaso Ya fice daga PDP, watakila ya koma ADC

– Babu Maganar komawar sa APC ❌

A kwanakin baya Jaridar Daily True Hausa ta buga labarin cewa kwankwaso da wasu jiga-jigan siyasa daga jam’iyyu daban-daban da kungiyoyi zasu kaddamar da sabuwar jam’iyya

Wadanda ake sa ran zasu kafa wannan sabuwar tafiya sun hada da:

1. Prof Pat Utomi 2. Dr Usman Bugaje 3. Engr Musa Rabiu Kwakwanso, 4. Farfesa Kingsley Moghalu, 5. Sanata Saidu Dansadau, (Shugaban, NRM) 7. Hadjia Najatu Mohammed, 8. Prof Remi Sonaiya, 9.Pastor Ituah Ighodalo, 10. Prof Osita Ogbu; 11. Dr Sadiq Gombe; 12. Comrade Promise Adewusi; 13. Chief Akin Braithwaite; 14. Arc Ezekiel Nya Etok; 15. Lady Khadija Okunnu-Lamidi; 16. Comrade Olawale Okunniyi dss.

Yan siyasan sun yanke wannan shawara ne a taron samar da sabuwar jam’iyyar da zatayi fito-na-fito na jam’iyyun PDP da APC ranar Lahadi a Legas.

Jam’iyyu da kungiyoyin da suka hallara sun hada da Rescue Nigeria Project, RNP; Nigeria Intervention Movement, ÑIM; Strategic Elements of the Civil Society Movement; Youths’ EndSars Movement, National Rescue Movement, NRM; da African Democratic Congress, ADC.

Sai dai a labarin da yake fitowa a halin yanzu, Tsohon gwamnan jihar kano mai wa’adi biyu, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da sauran jiga-jigan zasu sanar da makomar su a yau dinnan a gidan talabijin na Channel.

Karin bayani na nan tafe.

Related Articles

2 Comments

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button