Politics

‘Yar takarar gwamna a Adamawa ƙarƙashin jam’iyyar APC, Aisha Ɗahiru Binani ta nemi kotu ta hana INEC ‘soke nasararta ta zama gwamna’

‘Yar takarar gwamna a Adamawa ƙarƙashin jam’iyyar APC, Aisha Ɗahiru Binani ta nemi kotu ta hana INEC ‘soke nasararta ta zama gwamna’

‘Yar takarar gwamna a Adamawa ƙarƙashin jam’iyyar APC, Aisha Ɗahiru Binani ta shigar da ƙara gaban kotu tana neman umarnin wucin gadi game da dambarwa zaɓen jihar.

Tana dai neman Babbar Kotun Tarayya ta Abuja ne ta yi fassarar doka game da matakin da hukumar zaɓe ta ɗauka ranar 16 ga watan Afrilu, bayan an ayyana cewa ita ce ta yi nasarar zama gwamna, a zaɓen 18 ga watan Maris da kuma na cike-giɓi a ranar 15 ga watan Afrilu.

‘Yar takarar tana kuma neman kotu ta ba da umarni sannan ta hana INEC da jami’anta ɗaukar ƙarin wasu matakai na bayyana wanda ya yi nasara a zaɓukan da aka yi, har sai kotun ta yanke hukunci a kan buƙatar yin tsokacin shari’ar.

Mallam Ahmed Sajo, jami’i a kwamitin yaƙin neman zaɓe Sanata Aisha Binani ya shaida wa BBC cewa sun je kotu ne don a yi musu fassarar sashe na 149 na dokar zaɓe ta 2022.

“Sai an mata fassarar ma’anar dokar nan ta zaɓe, sashen da ya ce idan an rigaan ayyana ɗan takara ya ci zaɓe, to sai kotu ce kawai za ta iya warware wannan ayyanawar, ba hukumar zaɓe ko wani mutum ba” in ji Mallam Sajo.

Don haka ƙara na neman kotu ta dakatar da hukumar zaɓe yin duk wani abu har sai ta kammala wannan aiki.

Ahmed Sajo ya ce sashe 149 na dokar zaɓe ta 2022 ya bayyana cewa jami’n hukumar zaɓe ne kawai zai iya ayyana wanda ya yi nasara a wani zaɓe, kuma mutumin da ya ayyana Aisha Binani, jami’in INEC ne.

Dn haka, in ji shi, suke neman kotu ta yi musu bayani a kan shin idan jami’in INEC ya ayyana ɗan takara ko ‘yar takara a matsayin wanda ko wadda ta yi nasara a zaɓe, me doka ta ce?

Kwamishinan hukumar zaɓen jihar Adamawa, Barrista Hudu Ari ne, ya shiga zauren tattara sakamakon zaben a Yola cikin rakiyar ‘yan sanda a ranar Lahadi, inda ya ayyana Sanata Aishatu Binani ta APC a matsayin wadda ta lashe zaɓen.

Bai dai yi bayani filla-filla game da sakamakon da kowacce jam’iyya ta samu da kuma yadda aka ci zaɓen ba.

Matakin da ya sa INEC ta ce aikin da jami’in nata ya yi ya saɓa doka kuma haramtacce ne don haka ba za a yi aiki da shi ba.

Sai dai, Mallam Ahmed Sajo ya ce jami’in ya shaida musu cewa aikin da ya yi ranar Lahadi yana kan ƙa’ida “Don ya ce shi ne jami’in kula da zaɓe a jihar Adamawa.

Idan aka samu akasi a wurin waɗanda za su yi abin da ya kamata, shi yana iya yi, saboda kar a samu tsaiko”.

‘Ba a kan Binani aka fara ba’
Jami’in yaƙin neman zaɓen na Aisha Binani ya ce irin wannan al’amari ya taɓa faruwa a baya a ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, inda jami’in da ya kamata ya ayyana wanda ya yi nasara a zaɓe, ya ƙi zuwa.

Saboda haka in ji Ahmed Sajo jami’in zaɓe na wannan ƙaramar hukuma, ya tattara kuma ya zo ya ayyana wanda ya yi nasara kuma hukumar zaɓe ta amince.

An tambaye shi cewa amma a wannan al’amari na Adamawa, ba a kammala tattara sakamakon zaɓe ba, jami’in INEC ya sanar da mutumin da ya yi nasara.

Sai dai ya ce abin da ya faru shi ne wasu jami’an hukumar zaɓe ne suka je Adamawa, kuma suka ce sun dakatar da jami’in zaɓe, inda suka ce sun naɗa sabbin masu tattara sakamako.

A cewarsa, waɗanda INEC ta damƙa wa alhakin aikin tun farko sun kammala aikin tattaro sakamakon zaɓe, waɗanda aka canza daga bisani ne suka ce ba su gama aikin ba.

Ya ce “waɗanda za su ayyana wancan sakamakon zaɓe da ake cewa ba a kammala tattarawa ba, ai su ba halastattu ba ne”.

Ahmed Sajo ya yi zargin cewa hango faɗuwar da abokan takararsu suka yi ne ya sanya su canza jai’an zaɓe na ƙananan hukumomi.

Shin wanne hali ake ciki yanzu?
Kafofin yaɗa labarai a Najeriya sun ambato cewa hukumar zaɓe tana gudanar da wani taron sirri a tsakanin manyan jami’anta na ƙasa a hedkwatarta da ke Abuja.

Tun ranar Lahadi ne, INEC ta sanar da cewa tana kiran dukkan jai’an da ke da ruwa da tsaki a zaɓen gwamna na jihar Adamawa, don yin wani taron gaggawa a Abuja.

Sai dai a ranar Litinin kuma, INEC ta fitar da wata sanarwa inda ta dakatar da kwamishinan zaɓe na Adamawa, Hudu Yunusa-Ari kuma ta umarce shi ya fice daga ofishinta har sai an kammala bincike.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button