Religion

BIDIYO: An Sake Aikewa Da Sheikh Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi Gidan Kaso Saboda Tsaiko Da Aka Samu A Belinsa.

BIDIYO: An Sake Tura Sheikh Idris Gidan Kaso Saboda Tsaiko Da Aka Samu A Belinsa.

An tsare malamin ne bisa zarginsa da batanci ga manzon Allah a wani karatunsa.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da cece-kuce kan lamarinsa da kuma abin da ya yi.

BELIN SHEIKH DR IDRIS ABDUL-AZIZ BAUCHI

Alkalin Kotun Upper Shariah Court Bauchi Alkali Hussaini Turaki ya gindaya ka’idojin beli wa Sheikh Dr Idris Abdul-Aziz Bauchi guda uku:

(1) Dole Malam Idris Ya kawo wani Malamin addinin Musulunci sananne wanda yake da matakin karatun digiri na uku Dr, anan bangaren muna da Dr Ibrahim Disina

(2) Dole Malam Ya kawo wani dan kasuwa wanda yake da kudi sama da Naira Miliyan 10, a nan bangaren ma akwai daruruwan ‘yan kasuwa daliban Malam

(3) Dole Malam Idris ya kawo mai rike da sarautar gargajiya mai mukamin Hakimi, to anan ne inda gizo ke saka

A cikin wadannan ka’ido 3, guda daya ne zai bada matsala shine samun hakimin da zai sa masa hanu, saboda Hakimi yana karkashin Gwamnati ne

Amma duk da haka Alkalin yace zai yi tunani daga yau zuwa gobe, watakila ya rage ka’idar belin da ya gindaya wa Malam

Rayuwa kenan, komai da lokacinsa, watarana sai labari

Khairan Insha Allah

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button