Religion

BIDIYO: Kai Tsaye Daga Wajen Daurin Auren Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa A Zamfara

BIDIYO: Kai Tsaye Daga Wajen Daurin Auren Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa A Zamfara.

An daura auren Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa da amaryarsa mahaddaciyar AlQur’ani Mai Girma.

kuma wadda ta zama gwarzuwar wannan shekara (2022) a Musabaqar AlQur’ani ta kasa wanda ta gudana a garin Bauchi Hafiza Haulat Aminu Ishaq.

Sakataren kungiyar Izala na kasa Sheikh Muhammad Kabiru Haruna Gombe shine ya jagoranci ɗaurin auren a garin Gusau babban birnin Jihar Zamfara.

Bayan Kammala wannan daurin auren gwamnatin jahar ta shirya liyafar cin Abinci ga mahalarta wannan gagarumin biki.

Inda akaci akasha aka taya ango da addu’ar zaman lafiya da zuri’a dayyiba.

Haka zalika mutane da dama sun tayasu murna tare da addu’oin fatan alkhairi.

Musamman ma ma’abota shafukan sada zumuntar zamani, wanda anan ne labarin auren yafi daukar hankali.

Gadai bidiyon ku kalla

https://youtu.be/JvaptFnvb8I

 

Allah ya bada zaman lafiya, Ameen.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button