Religion

BIDIYO: Yadda Rasuwar Malama Rabi’atu Sufyan Uwar Marayu Akan Hanyar Ta Ta Zuwa Musabakar Karatun Al’qur’ani Ta Girgiza Mutane

BIDIYO: Yadda Rasuwar Rabi’atu Sufyan Uwar Marayu Akan Hanyar Ta Ta Zuwa Musabakar Karatun Al’qur’ani Ta Girgiza Mutane

Rabi’atu Sufyan: Tarihin fitacciyar Malamar addinin Musulunci da ta rasu

Jama’a masu dimbin yawa a Najeriya sun yi ta alhinin rasuwar fitacciyar malamar addinin Musuluncin nan Malama Rabi’atu Sufyan wadda Allah ya yi wa rasuwa ranar Asabar.

Bayanai sun nuna cewa Malamar ta rasu ne ita da wasu abokan aikinta na da’awa sakamakon hatsarin mota a yankin Samunaka na Jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya, yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa Musabakar Karatun Al-kur’ani mai girma a Jihar Adamawa da ke arewa maso Gabashin kasar.

Malamar ta yi fice wajen gudanar da wa’azi musamman ga mata a lungu da sakon Jihar ta Kaduna, da ma wasu sassan Najeriya.

Tuni dai aka yi jana’izarta a Kaduna.

A sakonsa na ta’aziyya da ya wallafa a shafin Facebook, Abu Aysha, ya bayyana marigayiyar a matsayin “uwar marayu, mai kamar maza wajen da’awa da taimaka wa al’umma.”

Wace ce Malama Rabi’atu Sufyan?
Wani ɗan jarida mai suna Adamu Garba da ya yi aiki sosai da malama kan harkokin da’awa ya shaida wa BBC cewa an haifi Malama Rabi’atu Sufyan kimanin shkeara 62 da suka gabata, kuma su uku ne a wajen mahaifiyarsu.

Tana da yaya Alhaji Yusuf wanda shi ma ya rasu, sai kuma ƙaninta Malam Sulaiman.

Ta rasu ta bar mahaifiyarta da ƙanin nata Malam Sulaiman.

Malama Rabi’atu Sufyan ƴar asalin ƙaramar hukumar Kura ce ta jihar Kano, kuma ta fara karatunta ne daga makarantar allo a can, daga bisani ta koma wajen kawunta a Lagos, “amma ba ta daɗe sosai ba sai ta koma Kaduna.”

Bayan wasu shekarau ta koma Jami’ar Ahmadu Bello Zaria inda ta yi digiri a fannin Larabci.

Kafin rasuwarta Malama Rabi’atu ma’aikaciya ce a gwamnatin jihar Kaduna a matsayin mai kula da makarantun firamare.

An fara sanin Malama Rabi’atu ne a lokacin da ta zama mamba ta ƙungiyar Da’awa ta mata ta Fomwan. Sannan ta zama mataimakiyar shugabar ƙungiyar Women In Da’awah.

Daga baya ta ƙiriƙiri tata ƙungiyar mai suna Initiative for Muslim Women in Nigeria IMWAN, kuma ita ce shugabar ƙungiyar ta ƙasa.

Malama ta yi aiki a matsayin jami’ar bayar da agajin gaggawa ta Jama’atu, ta yi mamba ta ƙungiyar MSS, sannan Sarkin Musulmi ya naɗa ta shugabar Gidauniyar Nana Asma’u ta ƙasa.

“Wani abin sha’awa shi ne malama ta rayu a kan neman ilimi da bayar da shi, kuma a kan wannan hanya Allah Ya karbi rayuwarta,” in ji Adamu Garba.

A lokacin gwamnatin Shugaban kasa Umaru Musa Yar’adua an gayyace ta gudanar da wadansu ayyuka da musamman da suka shafi mahajjata.

Malama tana yawan gabatar da shirye-shirye a gidajen rediyo da talabijin, daga cikin waɗanda suka fi fice har da wanda take yi a gidan talabijin ɗin Farin Wata mai taken “Mace Ta Gari”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button