Politics

BIDIYO: Ni da Shekarau muna tare Dari Bisa Dari – Kwankwaso

BIDIYO: Ni da Shekarau muna nan tare Dari Bisa Dari – Kwankwaso

Dan takarar shugaban Najeriya a jam’iyyar NNPP, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya ce babu wata matsala tsakaninsa da bangaren tsohon gwamnan Kano Sanata Ibrahim Shekarau.

A tattaunawarsa da BBC Hausa, Kwankwaso ya ce rahotannin da ake watsawa game da rashin jituwa tsakaninsa da bangaren Shekarau ba su da kamshin gaskiya.

Yana bayani ne bayan wasu rahotanni sun bayyana cewa Sanata Shekarau na shirin komawa jam’iyyar PDP saboda bangaren Kwankwaso ya gaza cika alkawuran da ya yi musu yayin da ya shiga jam’iyyar NNPP.

Sai dai Kwankwaso ya shaida mana cewa ko da yake shi ma ya samu wannan labari amma ba haka batun baye ba.

“Gaskiya babu wata yarjejeniya da aka yi da ta wuce cewa akwai bukatu da aka kawo kuma mun yi kokarin biyansu amma ba a kawo su a kan lokaci ba, kuma babu yadda za mu iya yi musamman abin da ya shafi takara,” in ji tsohon gwamnan na Kano.

A cewarsa, galibin wadanda bangaren Shekarau ya kawo domin su samu gurbin takara sun shiga NNPP a kurarren lokacin da INEC ba za ta amince da takararsu ba domin an kammala zabukan fitar da gwani.

Sai dai ya ce idan aka kafa gwamnati za su samu mukamai masu daraja.

Sanata Kwankwaso ya kara da cewa hakan ba zai haifar da wata matsala a jam’iyyar NNPP yana mai cewa babu matsala tsakaninsa da Shekarau.

Karin Bayani: 👇👇

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button