Politics

BIDIYO: Yanzu-Yanzu Kan Batun Komawar Kwankwaso Jam’iyyar NNPP Daga PDP

YANZU-YANZU: Kwankwaso na daf da sauya sheƙa zuwa NNPP

Tsohon Gwamnan Kano, Rabi’u Kwankwaso na daf da sake barin jam’iyar adawa ta PDP zuwa New Nigeria Peoples Party, NNPP.

Sakataren jam’iyar na ƙasa mai barin gado, Agbo Gilbert Major ne ya fasa ƙwai a kan shirin na Kwankwaso a yayin taron masu ruwa da tsaki na ƙasa da jam’iyar ke shirin yi a Abuja.

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Major ya ce tuni Kwankwaso ya gana da shugabannin jam’iyar domin tsara sauya shekar ta sa zuwa NNPP.

Ya ƙara da cewa yayin da a ke tunkarar kakar zaɓe ta 2023 a kasar nan, akwai bukatar a yi wa jam’iyar NNPP garambawul, inda ya ƙara da cewa ƴan siyasa da dama na kan hanyarsu ta shigowa jam’iyar.

https://youtu.be/947MOgN6TwU

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button