Politics

DA ƊUMI-ƊUMI: Jam’iyyar APC ta ki Tantance Tinubu, Saboda Shekarun Sa Na Bogi Ne Dakuma Yin Amfani Da Shedar Karatun Karya

DA ƊUMI-ƊUMI: Jam’iyyar APC ta ki Tantance Tinubu, Saboda Shekarun Sa Na Bogi Ne Dakuma Yin Amfani Da Shedar Karatun Karya

Dan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki, Sagir Mai Iyali, ya bukaci kwamitin tantance shugaban kasa na jam’iyyar da ya haramtawa daya daga cikin masu neman tsayawa takara, Bola Ahmed Tinubu takara bisa zarginsa da yin bogi.

An gabatar da karar mai kwanan wata 17 ga Mayu, 2022 a ranar Litinin, 30 ga Mayu, kuma wani Emmanuel Akpan ya amince da karbar ta.

Cancantar ilimi na Tinubu ya kasance batun cece-kuce sama da shekaru goma.

Ya bayyana cewa ya kammala karatunsa a Jami’ar Chicago a fom dinsa na INEC mai lamba 001 a lokacin da ya tsaya takarar gwamnan jihar Legas a shekarar 1999.

Tsohon gwamnan ya kuma yi ikirarin cewa a cikin takardar rantsuwar da ya makala a fom din INEC ya ce ya rasa shaidar kammala karatunsa na jami’a a lokacin da yake gudun hijira a tsakanin 1994 zuwa 1998.

Lauyan kare hakkin bil’adama, Cif Gani Fawehinmi (SAN), shi ma ya tuhumi Tinubu a kan sahihancin sa, ya kuma kai karar rundunar ‘yan sandan Najeriya bisa rashin bincikensa.

Kotun koli a hukuncin da ta yanke a ranar 10 ga Mayu, 2002, ta yanke hukuncin cewa ‘yan sanda ba za su iya gurfanar da Tinubu a gaban kuliya ba bisa zargin satar takardar shaidar jabu.

Kotun kolin ta kuma ce ba za a iya tursasa Sufeto-Janar na ‘yan sandan ya binciki Tinubu kan zargin sa da yin bogi ba saboda yana da kariya a lokacin yana gwamna.

A wata takardar koke da aka aike wa John Odigie Oyegun, shugaban kwamitin tantance shugaban kasa na jam’iyyar APC, an ce Tinubu bai kammala karatunsa a jami’ar Chicago ba.

Ya kara da cewa tsohon gwamnan ya yi karya game da shekarunsa da kuma yanayin asalinsa.

Dan jam’iyyar APC ya kara da cewa bai kamata a bar tsohon gwamnan Legas ya shiga zaben fidda gwani na jam’iyyar a ranar 7 ga watan Yuni ba.

“Mun fahimci cewa Bola Ahmed Tinubu wanda tun daga lokacin ya siyo fom dinsa na nuna sha’awa da tsayawa takara kuma ya mika wa jam’iyyar yana da wasu batutuwa da suka nuna a fili irin wannan yanayin na rashin cancanta.

“A tsawon shekarun da suka gabata, an boye sunan Asiwaju Bola Ahmed Tinubu. Hasali ma, ba wanda zai iya cewa ya san ainihin mutumin.

“Hakazalika, shekarun Tinubu ba kowa ne ya san shi ba, yana da mahimmanci a san ainihin shekarunsa, “in ji takardar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button