Religion

JIBWIS:Ta Magantu Kan Hotunan Dake Yawo A Media Na Shuwagabanninta Da Atiku Izala Ba Murna Ta Jewa Atiku Ba Ta’azaiyya Taje Yimasa Na Rasuwar Dan Sa Tun A Shekarar 2019

Izala Ba Murna Ta Jewa Atiku Ba Ta’azaiyya Taje Yimasa Na Rasuwar Dan Sa Tun A Shekarar 2019

Biyo bayan, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, daya lashe zaben fidda gwani na Dan takaran shugaban kasa. Karkahasin jam’iyyar PDP, Bisani jama’a suketa yin iso har gidansa a domin tayasa murna, ba dare ba rana.”

Bugu da kari, hakan ya kara bude wata sabon fai-faine, na ganin wasu hotuna da suke yawo a fadin yanar gizo na wasu daga cikin shuwagabannin Izala, da aka gansu a cikin gida tare da Atiku, cikin shaukin juna Da har jama’a suke tunanin wai kungiyar ta kaiwa Atiku ziyarar taya murnace toh” karyace! Kamar yadda Jaridar Alfijir Hausa tabi lamarin a bisa kididdiga da tsananta bincike kan wannan labarin.

Biyo bayan binciken da mukayi, mun gano cewa. Wadannan hotunan na shuwagabannin kungiyar Izala da aka hango su da Atiku din, an tabbatar mana cewa! Ta’aziyyace suka kaiwa Atiku Abubakar a tun shekarar 20219 na rasuwar Dan cikinsa.”

Hakan ya karawa wasu kafofin jaridu kaimi na wurin canza lamarin, yadda suka tsinkayi wadannan hotunan, suka kuma fake da hakan a domin cewa! Izala taje yiwa Atiku murnane don ya ci zaben fidda gwani, Aldijir Hausa tana kira da suji tsohon Allah su dakata da cigaba da yada wannan manufar”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button