Politics

Dan Ganduje ya yi barazanar maka mahaifin nasa a kotu kan Kin biyansa Kudinsa Miliyan 190, cikon kudinsa na kwangila

Dan Ganduje ya yi barazanar maka mahaifin nasa a kotu kan kin biyansa Miliyan 190, cikon kudinsa na kwangila

Jaridar Daily True Ta Rawaito Cewa, Babban dan gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, Abdulazeez Ganduje, ya yi barazanar gurfanar da gwamnatin mahaifinsa a gaban kotu bisa rashin biyan sa cikon kudinsa na aikin kwangila.

Lauyoyin Abdulazeez sun bukaci a biya su a cikin kwanaki bakwai ko kuma a fuskanci shari’a.

Da aka tuntubi Dan gwamnan, ya jaddada aniyarsa ta daukar matakin shari’a.

A baya Daily True Hausa ta buga labarin Abdulazeez Ganduje, ya taba maka mahaifiyar sa Farfesa Hamsat Abdullahi Umar Ganduje, ga hukumar nan dake Yaki da Yiwa Tattalin Arziki Tu’annati (EFCC).

Daga bisani EFCC din ta kama ta bisa wata takardar da Abdulazeez, daya daga cikin ‘ya’yanta ya rubuta kan badakalar cinikayya da mahaifiyar tasa tayi. Inji shi

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button