Religion

HAJJIN BANA: Bidiyon Jana’izar Ɗaya Daga Cikin Alhazan Jihar Nassarawa Da Ta Rasu A Makka

HAJJIN BANA: Bidiyon Jana’izar Ɗaya Daga Cikin Alhazan Jihar Nassarawa Da Ta Rasu A Makka

Hajjin bana: Ɗaya daga cikin alhazan Jihar Nassarawa ta rasu a Makka.

Shugaban Hukumar Jin dadin alhazai ta Jihar Nasarawa, Mallam Idris Ahmad Almakura ya tabbatar da rasuwar Hajiya Aisha Ahmad, ɗaya daga cikin mahajjatan jihar da ke ƙasar Saudiya domin aikin Hajjin bana.

Ya bayyana hakan ne a yau Laraba a lokacin da ya ke zantawa da manema labarai a birnin Makka.

A cewar Almakura, marigayiya Aisha, wacce ta fito daga Ƙaramar Hukumar Keffi a jihar Nasarawa, ta rasu ne bayan ta yi fama da gajeruwar rashin lafiya.

Shugaban Alhazan na Jihar Nasarawa ya bayyana cewa ta yi rashin lafiya kuma an garzaya da ita Asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makkah kafin ta rasu.

Kakakin hukumar, AbdulRazak ya shaidawa manema labarai cewa an yi jana’izar marigayiyar a makabartar Harami bayan sallar La’asar a jiya Talata.

Karin Bayani

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button