Religion

Hukunce-hukuncen Taimama Tare Da Comr Abdul M Adam

HUKUNCIN TAIMAMA

Tareda: Comr Abdul M Adam

Allah madaukakin Sarki yana cewa:

“وإن كنتم جنبا أو على سفر ولم تجدوا ماءا فتيمموا صعيدا طيبا وامسحوا بوجوهكم وأيديكم” الآية. (المائدة: 6).

“Wa’in kuntum junuban au ala safarin walam tajiduu maa’an fatayammamu sa’idan dayyiban wamsahuu biwujuuhikum wa’aydeekum…” (Al-Ma’ida:6)

Ma’ana: Idan kun kasance a halin Janaba, ko kuna halin tafiya baku sami ruwa ba, to kuyi taimama da kasa mai tsarki ku shafi fuskokinku da hannayenku”. (Surar Ma’ida Aya:6).

Taimama tana wajaba saboda rashin ruwa a halin tafiya. Haka ma tana wajaba idan ya zama akwai ruwan amma ba za’a iya tabashi ba saboda rashin lafiya.

Idan matafiyi ya tabbatar zai sami ruwa a gaba, to ya jinkirta sallah zuwa karshen lokaci, amma idan ya sakankance ba zai samu ruwa ba, to yai taimamarsa tun a farkon lokacin yai sallah, wanda kuma yake zaton zai samu ko ba zai samu ba, to yayi taimamar a tsakiyar lokaci.
Wanda yai taimama a cikin wadanda za’a ambata idan ya sami ruwa to ga hukuncinsa kamar haka:

1- Mara lafiya wanda bai sami wanda zai debo masa ruwa ba, har yai taimama yai sallah, idan ya sami ruwa lokaci bai fitaba, an so yayi alwala ya sake sallah.

2- Mai tsoron zakoki = Idan yaje inda ruwan yake akwai namun daji ko ‘yan fashi to daga baya sai wannan tsoron ya kau. Idan ya je ya debi ruwan kuma lokaci bai fitaba, shima an so yayi alwala yai sallah.

3- Matafiyi, wanda yake zaton ba zai sami ruwa a farkon lokaci ba, sai a karshe shima idan yai taimamar kuma sai ya samu a tsakiyar lokaci anso ya sake.

Ba’a sallar farilla biyu da taimama guda daya, sai dai kowace sallar farilla ai mata taimamarta daban.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button