Religion

Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji’un! Yanzu-Yanzu Muke Samun Rasuwar Babban Shehin Malamin Addinin Musulimci Shaykh Abdurrahman Umar Maigona (Rahmatul Laahi alaihi).

Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji’un! Yanzu-Yanzu Muke Samun Rasuwar Babban Shehin Malamin Addinin Musulimci Shaykh Abdurrahman Umar Maigona (Rahmatul Laahi alaihi).

Fitaccen Malamin Addinin Musulimcin Nan Wato Shaykh Abdurrahman Umar Maigona (Rahmatul Laahi alaihi) Ya Rasu.

 

Sanarwar Rasuwar Tasa Ta Fito Daga Fitaccen Malamin Addinin Musulimci Kuma Ministan Sadarwa Da Tattalin Arziki Wato Sheikh Ali Isa Pantami.

Wanda Ya Wallafa A Shafukansa Na Sada Zumuntar Zamani Kamar Haka.

Yanzu muke samun rasuwar abokin mu kuma aminin mu tun muna yara ‘yan ‘kanana, wato Shaykh Abdurrahman Umar Maigona (Rahmatul Laahi alaihi).

Wannan rasuwa tana da tsananin zafi gare ni. Kuma ba zan iya mantawa da ita ba har abada. Shaykh ya rasu ne, a Makkah, bayan kammala aikin hajji.

Muna rokon Allah, Ya gafarta masa, Ya sa Aljannah makomarsa, Ya albarkaci bayansa, Ya bawa magabatansa, lada mai yawa da hakuri mai kyau, Ya jikan dukkan magabatanmu, Ya hada mu dukkan mu a cikin Aljannah.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button