Religion

MASHA ALLAH: Kalli Bidiyon Yadda Mata da miji da suka yi fice a waƙoƙin Annabi tare

MASHA ALLAH: Kalli Bidiyon Yadda Mata da miji da suka yi fice a waƙoƙin Annabi tare

Duk da tarin mawaƙan yabon Manzon Allah Annabi Muhammadu S.A.W. da ake da su a ƙasar Hausa da duniya baki ɗaya, ba kasafai ake samun mata da miji na yin yabon a tare ba.

Wannan ta sa Hafiz Abdallah da matarsa Murja Bukhari Adam – wadda wasu ke kira da sunan mijinta – suka yi fice a fagen waƙoƙin yabon Annabi.

Ma’auratan, waɗanda ‘yan asalin Jihar Kano ne, malami ne da ɗalibarsa kafin su yi aure.

“Ni ɗalibarsa ce, tun a Islamiyya yake ban ƙasidu kuma da Allah ya tashi ikonsa sai ya haɗa wani abu mai girma – shi ne aure,” kamar yadda Murja ta shaida wa BBC Hausa game da mijinta.

Baya ga waƙa, Hafiz ya ce yana yin harkoki da dama, ciki akwai sayar da tufafi da harkokin man fetur da kuma dillancin tafiye-tafiye.

An haife shi a unguwar Kwanar Ɗiso da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a birnin Kano, kuma a nan ya taso.

‘Na fara rubuta waƙa ina shekara 10’
Malam Hafiz ya bayyana cewa tun yana ƙaramin yaro ɗan shekara 10 ya fara rubuta waƙoƙin yabon Annabi sakamakon baiwar da Allah ya yi masa, ba tare da tunanin zai zama mawaƙi ba.

Ya ce a lokacin da suke zuwa makarantar Islamiyya ne wani malaminsu mai suna Farfesa Hussaini Auwal ya ƙalubalanci ɗalibai da tambayar cewa wane ne zai iya rubuta waƙar yabo.

“Sai Allah ya ƙaddara ta hannuna wannan rubutun zai fito, na rubuta waƙar biyu na zo da ita aji bayan kwana ɗaya,” a cewarsa. “A lokacin ma ba na jin na cika shekara 10.

“To tun daga wannan lokacin ne abin ya ɗore har zuwa yanzu da muke magana da kai.”

Da take ba da labarin irin ƙalubalen da ta fuskanta a harkar yabon, Murja ta ce ɗaya daga cikinsu shi ne lokacin da mijinta ya kira ta a waya ya ce mata ya gama nasa baitocin a situdiyo, “ke ma ki zo ki ɗora naki”.

Ta ƙara da cewa hakan ya faru bayan mai gidan nata ya dawo daga aikin Umara a Saudiyya kuma ya wuce kai-tsaye zuwa ɗakin ɗaukar waƙar yana buga waƙar ‘Ambato’.

“Mu muna nan muna jiran ya ƙaraso mu tarɓe shi a gida, ashe shi ya wuce situdiyo. Sai kira na ya yi ya ce shi ya gama na zo na ɗora.

“Ka ga ban san amshin ba, ban san ya kiɗan yake ba amma da taimakon Allah da manzonsa ya gama na je na ɗora.

“Ni kam a kan wannan ba abin da zan ce sai dai na gode wa Allah.”

‘Lokacin da zan yi ritaya daga yabon Annabi’
Hafiz Abdallah ya ce rayuwa mataki-mataki ce kuma dole akwai abin da zan daina a yabo.

“Rera yabon Annabi, babu ranar da zan daina shi. Amma a cikinsa akwai abin da dole mutum sai ya bari,” a cewarsa.

“Misali, akwai matakin da idan mutum ya kai ya wuce a gayyace shi biki yau kan dandamali ya yi waƙa. Amma akwai lokacin da sai dai ka rubuta ka bai wa wani ya rera, ka saurara don ka ji daɗi. Wani lokacin kuma sai dai ka shiga ɗaki ka kunna kai kaɗai ka ji.

“Amma fita daga cikin da’irar Annabi, babu rana har abada.”

Soyayya ce ta sa nake yabon Annabi’
Mai yabon ya ƙara da cewa “ina son Annabi ƙwarai”, kuma abin da ya sa yake shirya waƙoƙin yabonsa ke nan.

“Za ka ga kowa yakan bi Annabi ne gwargwadon alfarmarsa a zuciyarsa – mai kuɗi ya hidimta masa da arzikinsa, malami ya hidimta da iliminsa. Haka shi ma mai hikima sai ya hidimta masa da hikimarsa.”

‘Babban alkairin da na samu’
Malama Murja ta ce babar nasarar da ta samu a rayuwarta sakamakon harkokin waƙar yabo ita ce zuwa ziyarar ƙabarin Annabi da ta yi a Madina.

“Na je na kuma zuwa, na kuma zuwa [ƙabarin Annabi Muhammadu S.A.W.] duk a sanadin yabon Annabi,” in ji ta. “Wannan ai ya fi komai girma.”

Kira ga masu yabo
Malama Murja ta ce kiran da za ta yi wa kan ta da sauran ‘yan uwanta masu yabo shi ne “a tsarkake zuciya kuma a nemi masana”.

Ta ci gaba da cewa: “Tafiyar Annabi sai an tsarkake harshe. Kamar yadda malamai ke faɗa mana sukan ce ka nemi ilimi kafin ka yi wa Annabi yabo saboda akwai kalmar da za ka faɗa wa Annabi da niyyar yabo amma idan aka fassara ta saɓanin haka ne.”

Shi ma Hafiz ya shawarce mawaƙa da cewa “a dinga neman shawarar malamai don a zauna lafiya”.

A cewarsa: “Ka san daga ina kake sannan ka san inda za ka je – wanda ilimi ne yake ba da wannan fassarar. A dinga tuntuɓar masana harkar rayuwa, waɗanda suke da ƙwarewa a harkar Annabi S.A.W.”

Ga Bidiyon Cikakkiyar Hirar

https://youtu.be/Lc9sdMc71NY

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button