Shugaba Muhammadu Buhari Zaje Katsina Domin Naɗin Dansa Yusuf Sarautar Talban Daura.
Wani Rahoto Da Muke Samu Daga Shafin Jaridar Rariya Na Cewa.
Ana Sa Ran Shugaba Buhari Zai Je Mahaifarsa Ta Daura Domin Naɗin Dansa Yusuf, Sarautar Talban Daura
A Ranar 18 Ga Watan Disamba, 2021 Ake Sa Ran Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Da Tawagarsa Za Su Bayyana A Mahaifarsa Ta Daura Dake Jihar Katsina.
Inda Za Su Halarci Bikin Naɗin Sarautar Dansa Namiji Daya Tilo, Yusuf Muhammad Buhari Sarautar Talban Daura.
Ana Sa Ran Wannan Biki Zai Samu Halartar Tawaga Ta Musamman Daga Fadar Shugaban Kasa.
Daga Jamilu Dabawa, Katsina