Politics

Ya kamata Buhari ya ɗaure ni da sauran ƴan siyasa saboda mun cuci Nijeriya — Tsohon Minista

Ya kamata Buhari ya ɗaure ni da sauran ƴan siyasa saboda mun cuci Nijeriya — Tsohon Minista

Tsohon Ministan Aiyuka, Ambasada Ibrahim Musa Kazaure ya ce ya kamata Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya kama shi da sauran ƴan siyasa da su ka rike madafun iko a ɗaure su sabo da sun zalunci ƙasar nan.

Da a ke zanta wa da shi a wani shiri a tashar rediyo ta Radio France International, Kazaure ya ce duk ƴan siyasar Nijeriya ɗaya su ke, inda ya ce babu wani wanda ya ke yi don talakawa.

A cewar sa, ya faɗa wa Shugaban Buhari da ya kame duk ƴan siyasar da su ka wawashe kuɗaɗen gwamnati har da shi.

Tsohon Ministan ya ce duk ƴan siyasan da su ka rike madafun iko tun daga 1999 ba su yi wa ƙasar komai ba.

“Har ni da na ke wannan maganar, ya kamata a ɗaure mu sabo da ba mu yi wa ƙasar nan komai ba

“Na sha faɗin cewa ni Ibrahim Musa Kazaure, mun zalunci Nijeriya da talakawan ta.

“Magana ta gaskiya ita ce, dukkan mu kanwar ja ce. Abin da mu ka yi wa Nijeriya ba haka ya dace mu yi mata ba sabo da wasu daga cikin mu sun samu dama wasu kuma basu samu ba.

“Ni dai gaskiya na faɗa. Dukkkan mu da mu ka yi sata, a matse mu mu dawo da kuɗaɗen da mu ka sata. Na faɗa wa Buhari, a kame mu a ɗaure mu har sai mun dawo da kuɗaɗen da mu ka sata.

“Ni ba zan sake karɓar wani muƙami a kasar nan ba, ko da kyauta ne,” in ji Kazaure.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button