Religion

BIDIYO: Ƴan Bindiga Sun Kashe Shugaban Ƴan Sanda Mai Kula Da Shiyyar Dutsinma (Area Commander) A Jihar Katsina

Ƴan Bindiga Sun Kashe Shugaban Ƴan Sanda Mai Kula Da Shiyyar Dutsinma (Area Commander) A Jihar Katsina

Ƴan Bindiga Dauke Da Bindigogi Sun Yi Wa Zakakurin Kuma Jajirtaccen Ɗan Sanda Mai Kula Da Shiyyar Dutsinma A Jihar Katsina.

DCP Aminu Umar Dayi Kwanton Bauna A Wani Daji Na Karamar Hukumar Safana A Jihar Katsina, Inda Suka Harbe Shi Har Lahira.

Majiyar RARIYA Ta Shaida Mata Cewa Ƴan Bindigar Sun Yi Masu Kwantar Bauna A Dajin Safana. Sun Kashe Shi Tare Da Ɗan Sanda Mai Tsaron Lafiyarsa Tare Da Kuma Wasu Ƴan Sa Kai.

Duk Kokarin Da RARIYA Ta Yi Na Ji Ta Bakin Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar, SP Gambo Isah Abun Ya Ci Tura Saboda Mun Buga Wayarsa Tana Karaurawa, Amma Ba’a Dauka.

Allah Ya Jiƙansu Da Rahama!

Daga Jamilu Dabawa, Katsina

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button