Religion

BIDIYO: Abinda Sarkin Fukaye Alhaji Mu’azu Kwairanga Na III Yayi Agabana Awanni 24 Kafin Ya Rasu. Sheikh Isa Ali Pantami

Abinda Sarkin Fukaye Alhaji Mu’azu Kwairanga Na III Yayi Agabana Awanni 24 Kafin Ya Rasu. Sheikh Isa Ali Pantami

A yau ne aka yi jana’izar marigayi Sarkin Funakaye da ke jihar Gombe a Arewacin Najeriya.

Sarki Mu’azu Muhammad Kwairanga na III ya rasu ne ranar Asabar da tsakar dare yana da shekaru 45 a duniya.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ya jagoranci ‘yan majalisar Zartarwarsa da dubban mutane wajen halartar sallar jana’izar Sarkin.

Sarkin ya rasu ne a ranar Asabar inda akai jana’izarsa a fadarsa da ke Bajoga, babban birnin karamar hukumar Funakaye.

Watanni 15 da suka gabata aka naɗa sarkin bayan mutuwar babban yayansa Alhaji Abubakar Kwairanga a ranar 20 ga watan Mayun 2021.

Ko a jiya Asabar sarkin ya halarci wani taro a birnin Gombe tare da ministan sadarwa, Farfesa Isa Ali Pantami.

Babu dai wasu bayanai da aka fitar kan abin da ya yi ajalinsa.

Sai dai gwamnan Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana mutuwarsa a matsayin babban rashi ga masarautar da jiha da kuma kasa baki daya.

A wata sanarwa dauke da sa hannun daraktan yaɗa labaran gwamnatin Gombe, gwamna Inuwa Yahaya, ya ce Gombe ta yi rashin ɗa wanda ke da nuna jajircewa wajen ayyukan ci gaba da hadin-kai da haɓɓaka.

Gwamnan ya mika ta’azziyarsa ga iyalan sarki da masarautar Funakaye baki ɗaya.

Marajiya Alhaji Muazu Muhammad Kwairanga III ana yi masa kallon matashin sarki da ke da nuna ƙwazo da himma wajen ayyukan al’umma.

Ga Bidiyon Ku Kalli Bidiyon

https://youtu.be/vDqKgFCMMuY

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button