Religion

BIDIYO: Duk Karyace Muke Yiwa Mutane, Auren Mace Fiye Da Daya Halas Ne: Rabaran Fada Ya Bayyana Yayinda Yayi Murabus

Duk Karyace Muke Yiwa Mutane, Auren Mace Fiye Da Daya Halas Ne: Rabaran Fada Ya Bayyana Yayinda Yayi Murabus

Mun Dade muna boyewa jama’armu gaskiya, Auren Mata Fiye Da 1 Halas Ne, Cewar Rabaran Fada.

Malamin addinin Kiristan ya yi murabus daga kujerarsa ta babban Bishop a cocin Anglican dake Nnewi

Fada Ogbuchukwu ya yi kira ga Maza su auri ‘yan matan da suke lalata da su don kada su shiga wuta rana gobe Kiyama

Wani babban Bishop na cocin Anglican dake Nnewi a jihar Anambra, Rabaran Fada Ogbuchukwu Lotanna, ya yi murabus daga kujerarsa a Cocin.

Rabaran Fada Lotanna, a jawabin murabus dinsa yace ya samu sabon umurni na ya kwadaitar da mutane kan auren mace fiye da daya don a rage zinace-zinace cikin al’umma, rahoton Punch

A cewarsa, auren mace fiye da guda ba haramun bane sabanin abinda ake tunani.

Yace Ubangiji na son mutane su auri mata fiye da daya maimakon neman matan aure da yan mata.

Yace Coci ta dade tana boye hakan ga mambobinta kuma lokaci ya yi da za’a fadawa mutane gaskiya.

Ya yi kira ga Maza su auri ‘yan matan da suke lalata dasu don kada su shiga wuta rana gobe Kiyama, riwayar TheNation.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button