BIDIYO: Masha Allah Yarinya Mai Shekaru 13, Mai Suna Zuwaira Ahmed Ta Haddace Kur’ani Tare Da Rubuta Shi A Jihar Katsina.
Wata karamar yarinya yar shekara goma sha uku a duniya ta haddace Al’kurani mai girma tare da rubuce shi.
Yarinyar mai suna Zuwaira Ahmed, An ruwaito cewa, ta samu wannan baiwa ne tun tana da shekara 5 Da Haihuwa.
Yayinda ta samu ikon sauke Al’qur’ani mai girma tare da rubuta shi kamar yadda aka wallafa a shafin sada zumunta.
Jaridar rariya ta rawaito cewa, Yarinya Mai Shekaru 13, Mai Suna Zuwaira Ahmed Ta Haddace Kur’ani Tare Da Rubuta Shi A Jihar Katsina.
To sai dai mutane nata yimata fatan Alkhairi tare da Addu’ar Allah yasa Kur’ani ya zamar mata gata.
A gefe guda kuma wasu naganin anya wannan abu zai yiwu kuwa, inda suke ganin kamar hakan zaiyi wahala a gareta