Religion

BIDIYO: Gwamnan Katsina Ya Dauki Nauyin Karatun Hafizar Alqur’ani Yar Shekara 13 Wadda Ta Rubata Alqur’ani Daka Har Sau Biyu

BIDIYO: Gwamnan Katsina Ya Dauki Nauyin Karatun Hafizar Alqur’ani Yar Shekara 13 Wadda Ta Rubata Alqur’ani Daka Har Sau Biyu

HARDAR ALQUR’ANI DA RUBUTA SHI

Gwamna Masari ya dauki nauyin karatun Zuwaira Ahmad a makarantar ARRAGHIBUN ACADEMY KATSINA

Sunan Yarinya

Zuwaira Ahmad Kagara

Shekarun Haihuwa

13

Gari

Kagara, Karamar Hukumar Kafur, Jihar Katsina

Sunan Makaranta

Tahfizul Qur’an Kagara

Sunan Malami

Sheik Sani Muhd Kagara

Tsawan Kwanakin Rubutu

Wata 2 da yan kwanaki

Karin bayan : Cikin ikon Allah munje garin Kagara mun isa gidan su Zuwaira tare da rakiyar Malaminta Sheik Sani mun same ta tana Rubuta AlQurani na biyu munyi hira da ita da mahaifinta. Tana da baiwa matuka saboda da ka ta rubuta AlQurani na farko haka na biyu da muka same ta tana yi da ka.

Gwamnan jihar Katsina Alh Aminu Bello Masari ya dauki nauyin karatun Zuwaira Ahmad a sabuwar makarantar nan wadda Alh. Muhd Sanusi Wada Rahusa ya assasa, makarantar wadda take da kwarrarun Malamai da kuma wadattatun kayan aiki.
Tuni dai Zuwaira ta baro gida ta tafo makaranta kamar yadda ku ke gani a cikin wannan hotuna.

Za ku iya ganin hoton Alqur’anin farko da ta rubuta a hannun Mai Girma Danejin Katsina Sheik Bello Abdulkadir Yammama.

Hk Yaradua
30/10/2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button