BIDIYO: Nayi Aikin Hajji Naje Dubai Sanadin Musabakar Alqur’ani Mai Girma- Hafeeza Aisha Hassan Abubakar

Ɗalibar nan ƴar Kano Aisha Hassan Abubakar mai shekaru 19 da ta lashe musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa sannan ta zo ta 2 a musabaƙar mata ta Duniya ta bayyana yadda ta tsinci kanta a musabaƙar.

Aisha ta kuma bayyana burin da take da shi na karantar Medicine koda yake Jamb na ƙoƙarin yi mata ƙafa.

Kamar Yadda Zaku Kalli Bidiyon Yadda Akai Hira Da Ita A Tashar Freedome Radio Nigeria Dake Kano.

Dalibar Ta Baiyana Yadda Tayi Gwagwarmaya Har Ta Ciri Tuta Tare Da Daga Sunan Nigeria A Idon Duniya.

Kafin Lashe Wannan Gasa Ta Misabakar Mata Ta Duniya, Aisha Tasha Gwagwarmaya Dakuma Fadi Tashi A Neman Ilimi.

Duk Da Ta Hadu Da Kalubale Iri Iri, Amma Bata Sare Ba, Haka Taci Gaba Daga Inda Ta Tsaya.

Ga cikakkiyar tattaunawarta da Freedom Radio.

Click Here To Drop Your Comment