Religion

Bidiyon Shugaban da ke son a ɗauki matakai masu tsauri kan masu ɓatanci ga Annabi

Bidiyon Shugaban da ke son a ɗauki matakai masu tsauri kan masu ɓatanci ga Annabi

Firaministan Pakistan, Imran Khan, ya yi kira ga gwamnatocin ƙasashen yamma da su ɗauki mataki a kan mutanen da ke furta kalaman ɓatanci a kan Annabi Muhammad SAW, kamar yadda suke yi a kan waɗanda suka musanta kisan kiyashi da aka yi wa yahudawa.

Imran Khan ya ce Musulmi ba za su lamunci rashin girmama Manzon Allah ba.

Ya ce wadanda ke nuna ƙiyayya a ƙarƙashin inuwar ‘yancin faɗin albarkacin baki su nemi afuwa.

Yana magana ne bayan an kwashe kwanaki ana zanga zanga a faɗin ƙasar ta Pakistan ga magoya bayan wata jam’iyyar masu kishin Islama da ke fushi da yadda Faransa ke ƙarfafa ‘yancin wallafa zane-zanen ɓatanci na annabi Muhammad.

Duk da cewa a yanzu gwamnati ta haramta jam’iyyar (Tehreek-e-Labbaik Pakistan) amma Mista Khan ya bayyana ƙarara cewa ya yi tir da tarzomar da ta ɓarke akan tituna.

Wasu ƙasashe sun bayanan ƙaryata kisan kare dangin da aka yi wa yahudawa a matsayin babban laifi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button