Religion

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un;! Yanzu-Yanzu Allah Yayiwa Daya Daga Cikin Mahajjatan Jahar Kaduna Da Basu Dawo Ba Rasuwa.

Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju’un;! Yanzu-Yanzu Allah Yayiwa Daya Daga Cikin Mahajjatan Jahar Kaduna Da Basu Dawo Ba Rasuwa.

Kamar Yadda muka samu rahoton daga Umar Shehu Zaria Wanda Ya Wallafa A Shafin Sada Zumunta Cewa.

Dazu kenan yayin da aka Gudanar Janaizar daya daga cikin Mahajjatan mu na jihar Kaduna wato Hajia Maryam Ahmad daga karamar hukumar Igabi.

Andai Yi Jana’izar Tata Ne A Masallacin Haram dake Makkah a kasar Ta Saudi Arabia.

Jana’izar ta samu halartan Shugabannin Alhazai na jihar Kaduna inda akai komai akan idonsu.

Allah ya ji kan ta da Rahma ya kyautata namu karshe

Tabbas rasuwa irin wannan rasuwa ce mai daga hankali, musamman ma ga iyalan wadanda sukai rashin.

Sai dai a gefe guda kuma Abin Alfahari ne da farin ciki ace mutum ya rasu a yayin ibadar Allah a dakin Allah Mai Tsarki.

Anan muma muke addu’ar Allah ya jikanta ya gafarta mata amin summa amin

#KDHAJJ2022

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button