Religion

Jama’a Nata Cece Kuce Tun bayan da aka Hango Wayar Samsung data Kai Kimanin (N1,250,000) a hannun Sheikh Kabiru Gombe.

Jama’a Nata Cece Kuce Tun bayan da aka Hango Wayar Samsung data Kai Kimanin (N1,250,000) a hannun Sheikh Kabiru Gombe.

Wani rahoto da ya karade shafukan sada zumuntar zamani, tare da janyo tafka muhawara tsakanin Al’umma Shine.

Batun wata tafkekiyar wayar hannu da aka hango ta maqudan kudade a hannun sheikh kabiru gombe.

Jama’a nata cece kuce a shafukan sada Zumunta inda aketa yada hotunan fitaccen malamin Addinin Musulunci watau Sheik Kabiru haruna gombe rike da wayar samsung data kai Kimanin kudi naira Miliyan daya da dubu dari biyu da hamsin (1,250,000) a hannun malamin.

Bayyanar wannan hoto dai yabar baya da Kura inda mutane da dama suketa tofa Albarkacin bakinsu, wasu na fadin cewa malam na rike wayar miliyoyin kudi haka? a yayinda wasu kuma suna ganin cewa wannan aiba wani abun magana bane kasancewar malamin ba ga malamta ya tsaya kawai ba.

Domin shima dan kasuwa ne kuma yasha bayyana hakan a wurare da dama cewa yana kasuwanci.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button