Religion

Ku Kalli Bidiyon Yadda Aka Kama Wani Alhaji Dake Damfarar Fulani A Kasa Mai Tsarki

Ku Kalli Bidiyon Yadda Aka Kama Wani Alhaji Dake Damfarar Fulani A Kasa Mai Tsarki

SUBHANALLAH: An Kama Wasu Gurbatattun Mutane Masu Damfarar Mahajjata A Yayin Aikin Hajjin Bana A Saudiyya.

Dubun wasu gurbatattun mutane biyu masu suna Abdullahi Adam Dala da Bashir Jibrin KMC ta cika, inda aka kama su suna damfarar mahajjata.

Saidai Bashir Jibrin ya gudu, yayin da shi kuma Abdullahi Adam Dala wanda ya shiga hannu, an kama shi da laifin damfarar wasu Fulani guda biyu da wasu mahajjata daga jihohin Kwara da Kaduna inda ya kwace musu daloli ya ba su dala daidaya.

Saidai alamu ya nuna cewa ‘yan damfaran ba ‘yan asalin Nijeriya bane, duba da yanayin harshen wanda aka kaman, kawai sun yi amfani da sunan jihar Kano a matsayin jihar da suka fito.

Ministar jinkai na Nijeriya, Hajiya Sadiya Faruk ita ta jagoranci kama mutumin tare da taimakon tawagar kungiyar Izala karkashin jagorancin Sheik Bala Lau, inda ta nuna bacin ranta matuka, ta kuma umarci da a kwace kudaden mutanen da suka damfara a maida musu da kayansu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button