Religion

Ku Kalli Bidiyon Yadda Wani Alhaji Bahaushe Ya Mayar Da Makudan Kudaden Da Ya Tsinta Na Wani Alhaji A Madina

Ku Kalli Bidiyon Yadda Wani Alhaji Bahaushe Ya Mayar Da Makudan Kudaden Da Ya Tsinta Na Wani Alhaji A Madina

Wani Alhaji Da Ya Fito Daga Jahar Sokoto Ya Mayar Da Zunzurutun Kudi Har Naira Dubu Dari Hudu 400, 000 Da Yan Tsinta A Madina.

Kamar Yadda Zaku Gani Acikin Bidiyon Dake Kasa, Shidai Wannan Alhajin Mai Suna Alhaji Arzika Bakaya.

Ya Mayar Da Zunzurutun Kudin Da Ya Tsinta Na Alhajin Jihar Kaduna Kamar Yadda Shafin Jaridar Aminiya Ya Rawaito.

Kudin Da Alhaji Arziki Ya Tsinta Dai, Sun Hada Da Dalar Amurka Dari Bakwai $700 Dakuma Kudin Nigeria Naira Dubu Saba’in 70.000 Dakuma Riyald 4 Na Saudia.

Rahotanni Sun Baiyana Cewa, Alhaji Arzika Ya Tsinci Wadannan Makudan Kudaden Ne A Kafar Benen Hotal Din Da Aka Sauke Su.

Haka Zalika Alhaji Arzika Ya Kara Da Cewa, Ko Kadan Baya Da Na Sanin Mayar Da Kudin Ga Ma Mallakan Su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button