Religion

Masha Allah: Wata Mata Ta Haihu A Masallacin Annabi S.A.W A Madina

Masha Allah: Wata Mata Ta Haihu A Masallacin Annabi S.A.W A Madina

Jami’an ƙungiyar agaji ta Red Crescent sun karɓi haihuwar wata mata da naƙuda ta tasar mata a Masallacin Manzon Allah da ke Madina.

Shafin da ke kula da masallatai biyu masu daraja na Saudiyya Haramain Sharifain ne ya wallafa labarin a shafinsa na Facebook a yau Juma’a.

Jami’an Red Crescent din sun je ne bayan kiran gaggawa da aka yi musu.

Bayan nan ne kuma sai aka kai mai jegon da jaririnta wani asibiti Jibril Health Center don ci gaba da kula da su.

Mahaifin jaririyar tuni ya raɗa mata suna Taiba, kamar yadda shafin ya ruwaito.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button